Galatians 2

Manzanni Sun Karɓi Bulus

1Bayan shekara goma sha huɗu sai na sāke haurawa zuwa Urushalima, a wannan lokaci tare da Barnabas. Na kuma tafi da Titus. 2Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Na bayyana musu bisharar da nake waʼazi a cikin Alʼummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yǎ zama a banza. 3Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi Bahelene ne. 4Wannan zance ya taso domin waɗansu ʼyanʼuwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ʼyancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi. 5Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku. 6Game da waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne-ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a wurina; domin Allah ba ya tāra-ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba. 7A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin waʼazin bishara ga Alʼummai,
Girik marasa kaciya
kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa.
Girik masu kaciya; haka ma a ayoyi 8 da kuma 9
kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa.
8Gama Allah wanda ya yi aiki cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Alʼummai. 9Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannun damansu na zumunci saʼad da sun gane alherin da aka ba ni. Sun kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Alʼummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa. 10Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.

Bulus Ya Tsauta wa Bitrus

11Saʼad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsauta masa fuska da fuska don laifinsa a fili yake. 12Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Alʼummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Alʼummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya. 13Sauran Yahudawa suka haɗa kai da shi a munafuncinsa har Barnabas ma ya bauɗe.

14Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai Bayahude ne, duk da haka kana rayuwa kamar Baʼalʼumme ba kamar Bayahude ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Alʼummai su bi alʼadun Yahudawa?

15“Mu da muke Yahudawa ta wurin haihuwa ba ‘Alʼummai masu zunubi’ ba 16mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka.

17“In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Almasihu, saʼan nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Almasihu yana ƙarfafa zunubi ke nan? Aʼa, ko kusa! 18In na sāke gina abin da na rushe, na zama mai karyar Doka ke nan. 19Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah. 20An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne kuma nake raye ba, sai dai Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina. 21Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!”

Copyright information for HauSRK